Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti kan zargin badakalar biyan Albashi

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin mai mutane tara domin gudanar da bincike kan zargin biyan albashi ga ma’aikatan kananan hukumomi su 379 da ba a tabbatar da sahihancin bayanansu ba.

 

Wannan dai na zuwa ne bayan gano batun yayin tantance albashi da aka yi ta hanyar raba takardu domin a duba ko bayanan albashi sun dace da na ofis.

 

Shugaban Ma’aikata na Kano Alhaji Abdullahi Musa, ya ce, kwamitin zai binciki ko ma’aikatan sun yi ritaya, ko sun mutu ko kuma ba a iya gane su ba ne.

Haka kuma ya ce, za kuma a nemo hanyoyin da za a hana irin wannan matsala a gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!