Labarai
Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin samar da zauren tsoffin ƴan jarida

Gwamnatin jihar Kano, ta kafa kwamitin da zai samar da zauren tsoffin ƴan jarida wanda zai fito da hanyoyin tsaftace al’amuran yada labarai.
Kwamishinan yaɗa labarai da al’amuran cikin gida Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya jagoranci kaddamar da kwamitin a Ofishinsa yau Alhamis.
Yayin kaddamar da kwamitin, kwamishinan ya ce, an kafa shi ne domin samar da wani zaure da zai fitar da ka’idoji da dokokin yada labarai a jihar Kano da nufin tsaftace harkar daga munanan kalamai da cin zarafi da kuma kauce wa kalaman da suka ci karo da tarbiyya da al’adun Bahaushe.
A nasa jawabin, shugaban kwamitin wanda ya kasance tsohon kwararren ɗan jarida Alhaji Ahmad Aminu, ya ce, kwamitin zai yi aiki tukuru domin fito da yadda zauren da za a kafa zai kasance.
Wakilan kwamitin sun hada da Alhaji Ahmad Aminu a matsayin shugaba da Alhaji Muhd Danyaro da Alhaji Abdulkadir Ahmad Kwakwatawa da Farfesa Umar Farouk Jibril.
Sauran sun hada da, Dakta Halima Musa Kamilu da Dakta Sule Yau Sule sai Dakta Saminu Umar Rijiyar Zaki a matsayin Sakatare da kuma Mustapha Gambo da Hauwa Sulaiman Zahraddeen a matsayin wakilai daga Kungiyar Yan jaridu reshen jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login