Labarai
Gwamnatin Kano ta kona jabun magunguna na fiye da Biliyan 1

Kwamitin yaki da miyagun kwayoyi da kwacen waya na Kano, ya kona jabun kwayoyi da kudin su ya kai Naira biliyan biyu da rabi.
Shugaban kwamitin Birgediya Janar Gambo Yar-aduwa mai ritaya, ne ya jagorancin aikin kona kwayoyin a hawan Kalebawa da ke yankin karamar hukumar Dawakin Tofa.
Shugaban ya kuma sha alwashin ci gaba da aikin yaki da masu tu’ammali da miyagun kwayoyi da kuma fadace-fadacen daba a fadin jihar Kano.
A nasa bangaren kwamishinan kimiyyya da fasaha na Kano Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata cewa ya yi gwamnati ta dauki matakin yaki da miyagun kwayoyi ne domin gyara tarbiyar matasan jihar.
Taron gangamin kona kwayoyin, ya samu halartar shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA shiyyar Kano Abubakar Idris Ahmed da sauran jami’an tsaro daga bangarori da dama.
You must be logged in to post a comment Login