Labaran Kano
Gwamnatin Kano ta rinka baiwa ‘yan jaridu hadin kai- Ammai Mai Zare
A yayin da ake bikin ranar Radio a fadin duniya a yau tsohon shugaban kungiyar ‘yan jaridu na jihar Kano Alhaji Ammai mai Zare ya bukaci gwamnati da ta rika baiwa ‘yan jaridu hadin kai a yayin da da suke neman labari.
Alhaji Ammai mai Zare ya bayyana haka ne a yayin taron kungiyar bunkasa ilimi da cigaban dumukuradiyya SEDSAC a wani bangare na bikin ranar radio ta duniya da ake gudanarwa a fadin duniya a yau.
Ammai Mai Zare ya kara da cewa, dokar kasa ta baiwa kowa damar samun bayanai akan ayyukan gwamnati wanda dama hakan shi ne babban aikin da ‘yan jaridu suka sanya a gaba, don sanar da al’umma halin da ake ciki.
Nassarawa:An sace tare da garkuwa da mai dakin shugaban kungiyar ‘yan jaridu
Ganduje ya hana iyayen yara Magana da yan jarida
Ofishin Akanta na Najeriya ya kalu balancida maganar wasu jaridu
Ammai Mai zare yace kafafan yada labarai sun yi matukar takarawa sosai wajen wayar da kan al’umma musamman wajen sanin hakkokinsu a gwamnati.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa, ‘yan jaridu daban-daban ne daga kafafan yada labarai suka halarci taron na kungiyar a yau sun kuma gudanar da jawabai akan muhimmancin radio ga alumma baki daya.