Labaran Kano
Gwamnatin Kano ta samar da na’urorin kama bata gari
Gwamnatin jihar Kano, ta gina babbar cibiyar sadarwa a shalkwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano da ke unguwar Bompai.
Rahotanni sun rawaito cewa, daraktan yada labaran gwamna Aminu Yassar na cewa, aikin ya kunshi kayayyakin sadarwa na zamani da wasu kayayyakin aiki na sabuwar fasahar zamani da kuma wasu kayayyakin more rayuwa, duk domin bunkasa harkokin tsaro.
Da yake jawabi yayin da ya kai ziyara cibiyar, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa an samar da wurin ne domin bibiyar mafakar bata gari tare da dakile matsalolin tsaro.
Haka kuma ya kara da cewa, matsalolin tsaro da ake fuskanta suna bukatar kulawa matuka tare da yin amfani da fasahar zamani domin ganin an shawo kansu.
Gwaman Ganduje ya kara da cewa, ba iya jihar Kano ce za ta amfana da na’urorin ba kadai wajen gano maboyar bata gari, har jihohin Jigawa da Katsina za su ci gajiyarta.
Ya kuma ce, gwamnatinsa ta samar da kayayyakin aiki na miliyoyin Naira a ofishin hukumar tsaro ta DSS, domin bibiya tare da dakile ayyukan bata gari a jihar Kano.