Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ganduje : zamu samar da kayayyakin aiki don yakar cutar COVID-19

Published

on

Gwamnatin jihar Kano tace zata tanadi dukkanin kayayyakin da jami’an kiwon lafiya zasuyi amfani dasu tare da kare Kansu  daga kamuwa da cutar Corona.

Gwamna Ganduje ne ya bayyana hakan yau yayin taron majalisar zartarwa na yau da ya zo da wani sabon salo inda ba’a gudanar da shi a dakin taro na council chamber ba kamar yadda aka sab aba a Afrika Haouse

Kasancewar yana daga cikin matakan kaucewa cunkuso da kuma kamuwa da cutar Corona da gwamnatin Kano ta dauka kan kare kai daga COVID- 19

Gwamna Ganduje ya kara da cewa sun fito da tsari da dokoki na musamman domin a tabbatar da cewa al’umma sun yi don kaucewa bullar cutar a jihar Kano.

Ya kuma kara da shawartar mutane wajen bin dokoki da aka gundaya musu domin kare lafiyar su.

Wakiliyar mu ta fadar Gwamnatin Kano Zahrau Nasir ta ruwaito cewa a yayin taron majalisar zartarwar na Yau yan majalisar zartarwar yanayin zaman su akwai tazara sosai a tsakanin su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!