Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kano ta sha alwashin kammala ayyukan da ta gaba
Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudurinta na kammala ayyukan da ta faro a sassa daban-daban na fadin Jihar nan.
Kwamishinan ayyuka Sufuri da Gidaje na Jihar Kano Injiniya Aminu Aliyu Wudil ne ya bayyana hakan yayin rangadin duba ayyukan da ake tsaka da gudanarwa a halin yanzu.
hanyoyin dai sun hada da gyaran Titin Kofar Waika daura da gidan zakka, da ginin dakunan karatu da zai dauki adadin dalibai 1500 a mazaunin din-din na Jami’ar Yusuf Maitama Sule, da kuma aikin magance zaizayar kasa a Barikin Sojojin sama na nan Kano.
Ya ce akwai bukatar jama’a su ci gaba da bada hadin kai wajen ganin an samu nasarar kammala ayyukan, tare da bayar da kyakkyawar kulawa kan ayyukan da gwamnati ke yi.
Da yake jawabi kwamandan Barikin Sojin sama na 455 Air Commodore Idris Sani ya bayyana jin dadinsa, duba da yadda zaizayar kasa ke ci gaba da cinye sassan Barikin.
Wakilin mu Umar Idris Shu’aibu ya ruwaito cewa yayin kewayen Kwamishinan ayyuka Sufuri da gidajen Injiniya Aminu Aliyu Wudil ya duba sabbin gine-gine a Makarantar gwamnati da ke garin Dawakin Tofa da kuma ginin gidaje a kauyen Ganduje da ambaliyar ta ruguje.