Labarai
Gwamnatin Kano ta soke Makarantun ‘Yan Mari
Biyo bayan karbar rahoton da kwamitin kwararru na sake duba yanayin karantun Almajirai a jihar Kano wanda Muhammad Tahar Adamu yake jagoranta gwamnatin Kano ta bada umarnin soke makarantun ‘Yan Mari.
A cewar Muhammad Tahar Adamu “Baba Impossible” gwamnatin Jihar Kano ta soke ayyukan gudanar da duk wani gidan Mari a nan Kano, saboda irin ayyukan da suke gudanarwa.
Shugaban Kwamitin sake fasalta tsarinAlmajiranci a nan Kano Dr Muhanmad Tahar Adam ne ya sanar da hakan a yau lokacin da da ya jagoranci zagayen ziyarar gani da ido da jami’an hukumarsa ke gudanarwa a nan Kano, don tantance yadda ake gudanar da gidajen ‘Yan Marin suke.
‘Yan mari 36 sun shaki iskar ‘yanci a Kano
Ko mene ne makomar ‘yan marin da ake sakowa?
Ganduje ya kaddamar da shirin makarantun Tsangayu da Al-qur’anai
Kazalika, Dr Muhammad Tahar Adam ya yi karin bayani kan cewa matakin bai shafi Makarantun Islamiyya da na Allo ba.
Har ila yau, kwamitin yace ya gano cewar ana take hakkin yara a wasu daga cikin irin wadannan makarantu na ‘Yan Mari.