Labarai
Gwamnatin Kano ta tura korafe-korafen da aka gabatar kan Malam Lawan Triumph ga majalisar Shura

Gwamnatin Jihar Kano ta aika da korafe-korafen da aka gabatar mata kan kalaman Malam Lawan Triumph zuwa ga majalisar Shura ta jiha domin ta yi nazari a kansu.
Wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun Sakataren Gwamnati Musa Tanko, ya fitar, inda ya bayyana cewa kungiyoyin addini daban-daban suka shigar da korafe-korafen, ciki har da Safiyatul Islam, Tijjaniya Youth Enlightenment Forum, da kuma wasu kungiyoyin Ahlul Sunnah da Qadiriyya.
Sanarwar ta rawaito cewa sakataren gwamnati Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya ce, gwamnatin jihar ta kuduri aniyar tabbatar da zaman lafiya da mutunta juna tsakanin mabiya addinai. Ya kuma roki jama’ar Kano da su kwantar da hankali su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum cikin bin doka da oda.
You must be logged in to post a comment Login