Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Hukumar karbar korafe-korafe a Kano ta kama tsohon MD na KASCO

Published

on

Hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta kama tsohon Manajan Daraktan Kamfanin samar da taki na jihar Kano (KASCO) Bala Muhammad Inuwa da zargi laifin karkatar da sama da Naira biliyan 4 mallakin gwamnatin jihar Kano.

A kwanakin baya ne dai hukumar korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce ‘ta fara binciken batan kudaden gwamnati a kamfanin samar taki na Kano (KASCO) da suka haura Naira Biliyan hudu tare da kwace wasu motoci da manyan motoci da taraktoci na noma.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai na hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Kabir Abba Kabir, ya fitar ranar Alhamis, a Kano.

A cewar sanarwar, an kama su ne bisa zargin karkatar da dukiyar jama’a, da kuma kalaman karya ko kuma dawo da sama da Naira biliyan 4 da gwamnatin jihar Kano ta warewa kamfanin samar da taki na Kano (KASCO) a matsayin tallafi.

Sanarwar ta Kuma ce, har ila yau, tana tsare da dan tsohon Manajan kamfanin Bala Inuwa Muhammad , wanda ya rattaba hannun a madadin mahaifinsa ne tare da karkatar da kudaden da suka kai N3, 275,685,742.00 ta hanyar asusun ajiyar wata kungiya dake da jigista da hukumar yiwa kamfanoni rijista.

“Haka kuma an karkatar da kudaden da suka kai Naira Miliyan 480 ta asusun ajiyar banki na wani kamfanin kasuwanci mai suna ‘Limestone Processing Link’ wanda yake karkashin jagorancin mai waccan kungiya, Inda aka yi amfani da shi wajen tura naira miliyan 400 zuwa asusun banki mai suna Bala Muhammad Inuwa.

Sanarwar ta kara da cewa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!