Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kano ta umarci masu shaguna a filayen gwamnati su kwashe kayansu

Published

on

Gwamnatin jihar Kano, ta umarci mutanen da ke da shaguna a filayen gwamnati da aka yi gini ba bisa ka’ida ba, da su tabbatar sun kwashe kayansu.
Gwamnatin ta bada umarnin ne ta cikin wata sanarwa da Sakatarenta Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya fitar a Alhamis din makon nan.
Ta cikin sanarwar, gwamnatin ta sanar da dukkanin masu kaya a shagunan da aka gina a jiki ko cikin makarantu ko Maƙabartu da Asibitoci da Masallatai ko gefen Badala da filayen ma’aikatu da Filayen wasanni da sauran wuraren shakatawa mallakin gwamnati da cewa su yi gaggawar kwashe dukkanin kayan su da ke cikin shagunan da aka gina a wadannan wurare ba tare da ɓata lokaci ba.
Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!