Labarai
Gwamnatin Kano ta umarci sabbin jami’anta su gaggauta bayyana kadarorinsu ga CCB

Gwamnatin Jihar Kano ta umarci sabbin jami’an da aka naɗa a muƙamai su gaggauta bayyana kadarorinsu ga hukumar ɗa’ar ma’aikata ta Najeriya Code of Conduct Bureau CCB.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim, ne ya bayyana haka a Kaduna yayin taron horas da manyan jami’an gwamnati a ranar Asabar.
Ya ce wannan mataki na daga cikin manufofin tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin gwamnati, tare da kare jama’a daga rikice-rikicen da suka shafi kudi da kuma tabbatar da gudanar da mulki na amana.
Ya ƙara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na ƙoƙarin tabbatar da cewa duk jami’an gwamnati suna aiki da tsoron Allah da riƙon gaskiya, inda ya bukaci sabbin jami’an su nuna kishin ƙasa ta hanyar bin wannan doka.
You must be logged in to post a comment Login