Connect with us

Labaran Kano

Gwamnatin Kano ta ware fiye da Naira biliyan biyu domin gina asibitoci a sababbin masarautu

Published

on

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnatin Jihar Kano ta ware fiye da Naira biliyan biyu domin ginawa sababbin asibitoci da karfafa wasu cibiyoyin lafiya a sababbin masarautu hudu da gwamnatin jihar Kano ta kirkiro a kwanakin baya

Gwamnatin ta jihar Kano zata gina asibitocin ne a masarautu hudu da ta kirkira a kwanakin baya da suka hada da Bichi da Gaya da Rano da Karaye.

Kwamishinan yada labarai Malam Muhammadu Garba ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a game da abinda majalisar zartarwar jihar Kano ta amince da shi.

Muhammad Garba ya kara da cewa gwamnatin ta jihar Kano zata kashe fiye da Naira biliyan 4 domin samar da kayan aiki a cibiyar kula da masu cutar daji.

Daga karshe Malam Muhammad Garba yace majalisar zartarwar jihar ta Kano ta amince da samar da kudade da suka kai Naira miliyan talatin domin karbar bakuncin taron majlisar matasa na farko a jihar Kano.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!