Labarai
Gwamnatin Kano ta yaba da shirin kasar Jamus na tallafa wa manoman shinkafa

Gwamnatin Jihar Kano, ta yaba da shirin gwamnatin kasar Jamus na tallafa wa manoman shinkafa kimanin mutane dubu goma sha biyu.
Kwamishinan harkokin Noma na Kano Dakta Danjuma Muhamud, ne ya bayyana haka a zantawarsa da wakilinmu Nura Bello.
Ya ce, gwamnatin Kano za ta yi tsayin daka wajen tabbatar da cewa al’ummar da aka yi wannan shiri dominsu sun amfana yadda ya kamata.
Haka kuma ya kara da cewa, tallafin zai taimaka wajen bunkasa harkar noma da rage talauci da kuma kara samar da abinci.
You must be logged in to post a comment Login