Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kano tayi Allah wadai da arangamar da aka samu tsakanin mafarauta a kauyen Ganduje
Gwamnatin jihar Kano ta yi Allah.. wadai da arangamar da aka samu tsakanin mafarautan kauyen Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum guda yayin da biyu suka samu munanan raunuka.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammadu Garba da ya fitar a jiya litinin, ta soki al’amarin da kakkausar murya, inda kuma ya ce tuni gwamna Abdullahi umar Ganduje ya umarci jami’an tsaro da su yi kwakwarran bincike kan musababin faruwar al’amarin tare da gurfanar da wadanda suke da hannu gaban kotu.
Ta cikin sanarwar, Malam Muhammadu Garba ya kuma yi watsi da yadda wasu masu san kansu, ke alakanta faruwar hakan da ziyarar da Gwamna Ganduje ya kai kauyen.
Ya ce wannan rigima tsakanin mafautan bata auku ba, har sai da gwamna ya bar kauyen, don dama ya je taron daurin aure ne.
Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa gwamnati bazata nade hannayen ta tana ganin irin wadannan matsaloli na kashe-kashen mutane na faruwa ba, don kuwa hakan babbar barazana ce ga tsaron jihar nan, tare da yin alkwarin daukar kwakwaran matakin dakatar da hakan.
Daga nan kuma sai sanarawar ta yi kira ga al’umma da su dauki dabi’ar hakuri da juna da kuma bin doka da oda domin tabbatar da zaman lafiyar jama’a.