Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kano tayi watsi da barazanar tsohon gwmna Rabiu Musa Kwankwaso
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi watsi da barazanar da tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ke yi na cewar zai kawo masa tarnaki wajen samun nasarar sa a zaben mai zuwa na 2019.
A cewar gwamnan ya bar ko mai a hannun Alla… kuma shi mulki All.. ne ke bada shi kuma yana baiwa wanda ya ga dama ne, a don haka babu wani mutum ko mai karfin sa da zai hana shi samun nasarar a zaben mai zuwa matukar All… ya bashi.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaran fadar gwamnatin jihar Kano Abba Anwar ya fitar da yammacin jiya Talata aka kuma rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ruwaito cewar gwamnan na wadannan kalamai ne lokacin da ya ziyarci guda daga cikin Dattijan jam’iyyar APC Malam Musa Gwadabe a wata ziyarar barka da Sallah.
Gwamnan ya ce duk wanda ya ce ya shirya domin tunkarar sa, to shi ma ya shirya domin tunkarar sa, inda ya bada tabbacin babu wata matsala cikin jam’iyyar APC a jihar nan.
Da yake mayar da jawabi Malam Musa Gwadabe ya bada tabbacin cewar dukkanin jam’iyyun da suka hade suka kafa jam’iyyar APC a shekarar 2015 suna tare da gwamnan a wannan karon ma.