Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kano tayi watsi da zargin cewar gina gadar Dangi baya ckin kasafin kudin bana
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana watsi da zargin da wasu mutane ke yi kan shirin ta na gina gadar sama a shatale-talen dangi inda suke cewa aikin baya cikin kasafin kudin bana da gwamnatin ta gabatar.
Kwamishinan yada labarai matasa da al’adu Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu, ya na mai cewa an tabbatar da aikin ne a zaman majalisar zartaswar jihar da ya gabata a kwanakin baya, da nufin samar da tituna masu inganci da za su kawo karshen cunkoso da ake fama da shi a cikin birnin.
Kwamishinan ya kuma ce, wasu mutane da kungiyoyin da wasu yan siyasa ke amfani da su da nufin kawo tsaiko kan gagarumin aikin titin dangin, irin su Hamisu Magaji sune ke ikirarin wai aikin baya cikin kasafin kudin bana.
Malam Muhammad Garba ta cikin sanarwar ya ce, gwamnati ware sama da Naira biliyan 4 da zummar gudanar da aikin wanda ya hadar da gadar kasa wacce za ta lashe kudi sama da biliyan 3 da miliyan talatin da biyu, wanda aka ware miliyan 150 daga ciki lokacin gabatar da kasafin kudi na shekarar da muke ciki.
Inda kuma kashi na biyu na aikin wato gadar sama zai lashe kudi sama da biliyan daya da miliyan dari hudu