Labarai
Gwamnatin kano za ta biya kudin karatun ɗaliban jihar da ke karatu a wasu jihohin
Gwamnatin jihar Kano ta ce zata biyawa ɗalibai dubu ashirin da hudu da ɗari da hamsin da daya kuɗin makaranta ga dukkanin ɗalibai ƴan asalin jihar Kano na makarantu goma sha biyu da suke arewacin ƙasar nan domin samar mu su da ci gaba da karatun su musamman ga wa’inda aka kasa biya musu kuɗin.
Shugaban hukumar bayar da tallafin karatu na jihar kano Alhaji Kabiru Getso Haru ne ya bayyana hakan a safiyar yau yayin taron manema labarai da ya gudanar inda ya ce la’akari da Yadda wasu iyaye suka kasa biyawa ƴaƴan su kuɗin makarantar yasa gwamnati ta ce zata biya mu wannan kudin domin ci gaba da karatun su.
Kabiru Getso ya ce a baya gwamnatin ta biyawa dalibai kuɗin makaranta iya mallakin ta, adan haka yanzu haka gwamnati ta bayar da umarnin fara tantance daliban ƴan asalin jihar Kano da suke a makarantu 12 da suke arewacin ƙasar.
Dakta Kabiru Getso Haruna ya bayyana makarantun kamar haka.
Kwalejin koyar da aikin Noma ta tarayya dake hotoro, jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa dake Bauchi, Jami’ar Maiduguri,Jami’ar tarayya ta Gusau da kuma Dutsen ma sai jami’ar Sule Lamido dake kafin hausa, da kuma jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, sai jami’ar Tarayya ta jihar Gombe, da kuma kwalejin tarayya dake kano FCE, sai kuma Usman Danfodiyo dake Sokoto da kuma jami’ar umaru musa dake katsina.
Haka kuma ya ƙara da cewa iya wannan karon kaɗai gwamnati zata biya domin taimakon gaggawa ga ɗalibai kar kowa ya zata gwamnati zata ci gaba da biya musu kuɗin makaranta.
Ka zalika gwamnatin jihar Kano ta ce nan gaba za ta ci gaba da tantance ɗalibai domin basu tallafin karatu kamar yadda aka saba
You must be logged in to post a comment Login