Labarai
Gwamnatin Kano za ta haɗa gwiwa da Ghana don farfaɗo da ilimi
Gwamnatin jihar Kano, ta ce, za ta yi haɗin gwiwa da ƙasar Ghana domin farfaɗo da harkokin ilimi.
Gwamnan Kano jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi baƙuncin ƙaramin ministan lafiya na ƙasar ta Ghana Alhaji Mahama Ase Asesini, wanda ya kai ziyara gidan gwamnatin Kano.
Abba Kabir Yusuf wanda ya kuma bayyana tsohuwar dangantakar da ke tsakanin alumar jihar Kano da kasar Ghana, yace gwamnatin kano zata farfado da dangantakar ne domin amfanar da alumar kasashen biyu.
Gwamnan, ya ƙara da cewa, gwamnatinsa za ta gyara tare da samar da isassun kayan aiki a dukkan manyan asibitocin da ke ƙananan hukumomin Kano 44.
Da ya ke jawabi tun da farko, ƙaramin Ministan lafiyan na Ghana Alhaji Mahama Ase Asesini, ya ce, ya kai ziyarar ne domin farfaɗo da dangantar da ke tsakanin Kanawa da mutanen Ghana ta furskar al’adu da zamantakewa.
Rahoton: Umar Abdullahi Sheka
You must be logged in to post a comment Login