Labarai
Gwamnatin Kano za ta hana ajiye manyan motoci a titin Dawanau

Gwamnatin jihar Kano ta ce, za ta hana masu manyan motocin dakon kayan abinci tsayawa akan titin kasuwar Dawanau biyo saboda yadda suke haddasa cunkoso tare da haifar da hatsari a kan titin.
Kwamishinan harkokin Sufuri nl kano Ibrahim Ali Namadi Dala, ne ya bayyana hakan yayin da ya kai ziyara sabon filin da aka ware domin tsayawar motocin, inda ya ce, wannan tsarin da gwamnatin Kano ta fito da shi zai taimaka wajen ƙara samarwa da matasa aikin yi.
A nasa jawabin shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa Anas Bello Danmaliki ya ce, kaddamar da filin zai bai wa manyan motocin dakon kaya damar tsayawa yin fakin
Haka kuma gwamnatin ta sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da karya dokar ajiye manyan motoci a kan hanyar.
You must be logged in to post a comment Login