Kiwon Lafiya
Gwamnatin Kano za ta ƙaddamar da aikin kashe Ɓeraye

Gwamnatin jihar Kano, ta ce, za ta kashe Ɓeraye a karamar hukumar Garun Malam domin dakile yaduwar cutar zazzaɓin Lassa.
Kwamishinan Lafiya na jihar Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran ma’aikatar lafiya Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa fitar.
Sanarwar ta ce, ya zama dole gwamnati ta dauki wannan mataki na gaggawa domin kare lafiyar al’umma, ganin yadda aka tabbatar da bullar cutar Lassa a Garun Malam, wadda ta yi sanadin rasuwar wata mata.
Kwamishinan ya bayyana cewa tuni aka killace duk wadanda suka yi mu’amala wadda ta, rasu din, ciki har da mijinta da kuma jami’an lafiyar da suka kula da ita lokacin da aka kai ta asibiti.
Ta kuma ruwaito cewa, “Binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa mijin marigayiyar da daya daga cikin yaranta sun kamu da cutar”.
“Dakta Abubakar Labaran, ya jaddada cewa kashe Ɓerayen da ke yankin da abin ya shafa wani muhimmin mataki ne na dakile yaduwar cutar, kasancewar Ɓeraye na daga cikin manyan hanyoyin yada cutar Lassa.”
“Gwamnatin ta kuma ja hankalin mafarauta da su guji farautar Ɓeraye, da kuma daukar matakan kariya domin hana yaduwar cutar daga jikinsu zuwa ga mutane, inji sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa, Kwamishinan ya shawarci jama’a da su rika hanzarin sanar da jami’an lafiya mafi kusa idan suna da wani zargin cutar Lassa, tare da umartar jami’an lafiya da su dauki matakan kariya yayin da suke kula da masu fama da cutar, domin kauce wa yada ta.
You must be logged in to post a comment Login