Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta shawarci masu zuba hannun jari a Kano

Published

on

Kotun hannayen jari ta kasa shiyyar Kano, ta ja hankalin mutane masu bukatar zuba hannun jari a kamfanoni daban-daban da su tabbatar da sun yi bincike sosai kan kamfani kafin su zuba kudadensu a ciki.

Babban Magatakardan Kotun ta kasa, Barista Habu Yarima Saleh ne ya bayyana hakan yau ta cikin shirin Duniyar Mu A yau na nan Freedom Rediyo wanda ya maida hankali kan yadda a ke gudanar da kasuwancin hannayen jari bisa tsari da kuma doka.

Barista Habu Yarima ya ce gudanar da bincike game da kamfanoni zai bawa mai bukatar sayan hannun jari, damar samun bayanan kamfanin da suka danganci rijistar sahalewar hukumar yiwa kamfanoni rigista ta kasa wato (CAC) ko da wata matsala ka iya biyo baya.

Babban Magatakardar ya ce daga shekarar 2003 zuwa yanzu kotun ta karbi korafe-korafe daga wurin jama’a kan sayen hannayen jari a kamfanoni daban-daban da ya kai kimanin naira biliyan dari uku da casain.

Labarai masu alaka:

kasuwar hannun jari kasuwa ce da bata da tabbas a bangaren farashi

Kai tsaye : Sarkin Kano na karbar tawagar masu zuba jari daga kasar China

Barista Habu Yarima ya kara da cewa, kasuwar hannayen jari kasuwa ce da bata da tabbas a bangaren farashi, ta yadda ake iya samun hawa da sauka ako wane lokaci, wanda hakan shi ke kawo yawaitar matsaloli daga bangaren masu zuba hannayen jarin.

A nasa bangaren, Babban Sakataren kotun shari’ar hada-hadar hannayen jari dake nan Kano, Barista Kabiru Kiru da ya kasance a cikin shirin ya bayyana cewa sakacin mutane na rashin cikakken bincike ke jefasu hannun yan damfara da sunan zuba hannun jari.

Ya ce ya kamata mutane su sani cewa babu wani kasuwanci da yake kawo irin ribar da za ta ninkawa mutum kudinsa cikin dan kankanin lokaci kamar yadda wasu baragurbin kamfanonin hannun jarin ke yi wa mutane alkawari.

Baki dayan bakin sun yi kira ga alumma da suke da niyyar zuba hannun jari a wani kamfani da su rika neman shawarari ga masana a bangaran.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!