Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano za ta kwashe masu lalurar kwakwalwa da ke gararamba a kan tituna

Published

on

Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Kano (SEMA), Isyaku Abdullahi Kubaraci, ya ce hukumar ta gano yawan mutanen da ke fama da matsalar tabin hankali da ke yawo a tituna da unguwanni daban-daban na johar Kano, wadanda gwamnatin baya ta yi watsi da su.

A zantawarsa da Freedom Radio Kubaraci, Ya ce rahoton da suka tattara ya nuna cewa rashin daukar mataki a baya ya jawo karuwar mutanen da ke garari a titi, lamarin da yake kai su cikin hadari da kuma haifar da fargaba ga al’umma. A cewarsa, da dama daga cikinsu suna bukatar kulawar likitoci da wurin jinya, ba zargi ko kuma hukunta su ba.

ya kuma ce sabuwar gwamnati ta fara shirin tattarawa, tantancewa da tura su cibiyoyin jinya tare da yin aiki da ma’aikatar lafiya da hukumomin tsaro. Ya kuma bukaci jama’a su rika sanar da hukumomi idan sun ga irin wadannan mutane domin taimakon su a kan lokaci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!