Connect with us

Labaran Kano

Gwamnatin Kano zata sabunta tallafin ilimi na shekara 5 da kasar Faransa

Published

on

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnatin sa zata sabunta yarjejeniyar ilimi tsakaninta da gwamnatin kasar Faransa, karkashi tallafin ilimi na Kano da Faransa, na shekaru 5 wanda zai fara aiki daga shekara ta 2020.

An dai fara wannan yarjejeniya ne a shekara ta 2016.

Gwamnan ya ce Karin na shekaru 5 da aka samu a yanzu, domin baiwa daliban da zasu cigaba da digirinsu na uku, damar cigaba da karatunsu,ko da kuwa basu sami damar kamala karatunsu ba a zangon farko.

Wannan dai na kunshe cikin wata sanarwa da sakataren gwamna Abba Anwar ya fitar a jiya.

Sanarwa ta yaba da tsarin ilimin tsakanin gwamnatin Kano da gwamnatin Faransa, inda ya ce wannan wani shiri na inganta harkar ilimi.

Ya ce a cikin shirin alal misali an tsari shi ne domin inganta malaman jami’oi wanda zasu dawo gida su kuma inganta harkar koyarsu ga dalibai a nan gida.

Gwamna ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyara ga dalibai jihar Kano wanda suka samu tallafin karatu suke kuma kasar ta Faransa, a birnin Paris a jiya, ya kara da cewa gwamnatinsa na kokarin  inganta ilimi a dukkanin matakai.

Ganduje ya kara da cewa ya zama wajibi ayi wa harkar ilimi garanbawul , tun daga tushe a don haka ne aka mayar da ilimin ya zama kyauta kuma dole ga dukkanin yan makarantar firamare da sakandare.

Wanda tuni aka fara aiwatar da hakan, a wani yunkurin samar da dalibai masu kwazo a firamare da sakandare, a yanzu kuma ake kokarin inganta makarantar gaba da sakandare.

Da take Magana wata daliba da take koyon aiki a ofishin jakadancin Faransa a Najeriya Mrs Laila Matthew ta bukaci gwamna Ganduje da hallarci ranar Najeriya da za’a gudanar a  Faransa inda yan Najeriya da suke neman ilimi a Faransa daga jami’oi daban-daban zasu gana  wasu dalibai na faransa domin karawa juna sani.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!