Kiwon Lafiya
Gwamnatin kano zata sake nazarin kwangiloli saboda tashin firashin kayayyaki
Gwamnatin Kano ta sake jadada kudirin ta wajen samar da hanyoyi a cikin jihar nan.
Kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri Injiniya Aminu Aliyu ne ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyarar gani da ido titin Gidan Maza na Bye-pass dake karamar hukumar Kumbotso da kuma na Gwarmai dake karamar hukumar Bebeji da ake kan aikin gina su
Injiniya Aminu Aliyu ya ce bisa rokon da dan kwangilar dake gina titin Bebeji ya yi, ya sanya gwamnati ta sake nazarin kwangilar saboda yadda firashin kayayyaki suka tashi , yana mai cewar aikin gina titin zai lankwame fiye da Naira biliyan guda kuma ya kai tsayin kilomita 14.
Da yake jawabi shugaban karamar hukumar Bebeji Alhaji Ali Namadi ya bayyana jin dadin sa kan aikin gina titin ya kuma yi kira ga al’umma da su mara wa dan kwangilar baya wajen gudanar da aikin sa
Wannan na kunshe cikin sanarwar da jami’in yada labarai na ma’aikatar Mustapha Ahmad Nuhu ya sanya wa hannu cewa, Alhaji Aminu Dantata ne ya gina titin na Gwarmai dake karamar hukumar Bebeji tun a shekara ta 1982.