Labarai
Gwamnatin Kano zata samar da jakadun wayar da kai
Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin samar da jakadun wayar da kai na al’umma wato Education Vanguard , a mazabu 484 dake fadin jihar Kano don tabbatar da ingancin shirin ta na Ilimi wajibi kuma kyauta a jihar.
Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, Muhammad Sunusi Sa’id Kiru, ya bayyana haka ga yan Jaridu a wata ganawa ta musamman da ya yi dasu a ma’aikatar Ilimi ta jiha.
Muhammad Sunusi Sa’id Kiru, ya kara da cewa gwamnati ta fito da sabbin tsare tsare , da zata hada kai da kungiyoyin kasashen Ketare dake bada tallafi a harkokin Ilimi, don ganin an samar da wadatattun ajujuwa , Malamai da sauran kayan aiyyukan gudanar da makarantun bisa tsari dai dai da Zamani.
Muhammad Sunusi Sa’id Kiru, ya ce duk da an samu tsaiko na rashin isar kudaden gudanar da tsarin Ilimi kyauta ga wasu makarantun sakamakon matsaloli daga Bankuna, da basu tura kudaden ba, hakan ba zai sa suyi kasa a gwiwa ba wajen ganin kowacce makaranta ta samu nata kason don aiwatar da tsarin.
Gwamnatin Kano zata sabunta tallafin ilimi na shekara 5 da kasar Faransa
Gwamnatin Kano zata fara aiwatar da tsarin asusu bai daya a shekara ta 2020
Gwamnatin Kano zata fara aiwatar da tsarin asusu bai daya a shekara ta 2020
Wakilin mu Aminu Halilu Tudun Wada, ya ruwaito mana cewa gwamnatin tasha alwashin cewa zata rage cunkoson dalibai a ajujuwa, tare dayin duk mai yiwuwa don ganin ta raba Mata da yara masu tallace -tallace da gararamba a tituna na jiha, ta hanyar maida su makarantu don samun Ilimi na Zamani da na Addini.