Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Tsaro

Gwamnatin Katsina ta sha alwashin samar wa yan sanda kayan aiki

Published

on

Gwamnatin jihar Katsina, ta ce za ta tallafa wa ‘yan sanda da kayan aikin da suka dace domin wanzar da zaman lafiya a lokacin zabe da bayan gudanar da shi. 

Gwamnan jihar Aminu Bello Masari, ne ya ba da tabbacin lokacin da ya karbi bakuncin sabon mataimakin babban sufeton ‘yan sanda Ahmed Abdulrahamn, mai kula da shiyya ta 14 da aka tura jihar da ta kunshi jihohin Katsina da Kaduna.

 

Gwamna Masari ya ce, jihar Katsina na bukatar karin jami’an ‘yan sanda domin samar da tsaro yadda ya kamata

 

Haka kuma, ya yi wa mataimakin babban sufeton ‘yan sandan fatan samun nasara wajen gudanar da aikin sa.

 

A nasa jawabin Ahmed Abdurahman, ya ce, zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin an samu wadataccen tsaro yayin gudanar da zaben gwamnoni da ke tafe.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!