Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun kai mutane 9 kotu bisa zargin su da sayan kuri’a yayin zabe- EFCC

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC shiyyar Kano, ta ce, ta kama mutane da dama bisa zargin su da aikata laifin sayen ƙuri’u da raba kayan abinci domin a zaɓi jam’iyyun su.

shugaban hukumar shiyyar jihohin Kano da Jigawa  da kuma Katsina Faruk Dogon Daji, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawarsa da Freedom Radio.

Haka kuma ya kara da cewa, tuni hukumar ta miƙa mutane tara kotu cikin wadanda ta cafke din a jihohin Kano da jigawa da Katsina.

Faruk Dogon Daji ya kara da cewa hukumar ta EFCC, ta shirya tsaf wajen ganin an gudanar da zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi lami lafiya.

Kunna Bidiyon kasa domin kallon cikakkiyar tattaunawar.

https://www.youtube.com/watch?v=BNp9vy6biPg

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!