Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kogi ta tabbatar da ceto mutum da aka sace yayin jarrabawar NECO

Published

on

Gwamnatin jihar Kogi ta ce jami’an tsaro sun ceto mutum huɗu da aka sace yayin wani hari da ƴan bindiga suka kai wata makaranta a ƙaramar hukumar Dekina.

An sace ɗaliban ne tare da shugaban makarantar da kuma wani ma’aikacin wucin gadi na hukumar shirya jarabawar NECO a ranar Talata, bayan da wasu ɗauke da makamai suka kai hari makarantar da ke Odo-Ekina.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kingsley Fanwo ne ya tabbatar da ceto mutanen a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce an ceto su ne bayan wani samame na haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka ƙaddamar bisa umarnin gwamna Usman Ododo.

“Mun tabbatar da cewa an saki shugaban makarantar da jami’in NECO da kuma ɗaliban biyu, kuma duk suna cikin ƙoshin lafiya,” in ji sanarwar.

Fanwo ya ƙara da cewa halin yanzu suna hannun jami’an tsaro domin ɗaukar bayanansu da kuma yi musu gwaje-gwajen lafiya da suka kamata.

Ya kuma ce: “Har yanzu jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da samame a cikin dajin domin kamo waɗanda suka kai harin.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!