Connect with us

Labarai

Gwamnatin Yobe ta ware fiye da miliyan 460 don tallafa wa mata masu kananan sana’a

Published

on

Gwamnatin jihar Yobe ta amince da kashe Naira miliyan 460 da dubu 828 da 450 domin tallafa wa mata masu ƙananan sana’o’i, ciki har da masu soyar ƙosai.

 

An amince da hakan ne a taron Majalisar Zartarwar jihar da Gwamna Mai Mala Buni ya jagoranta a Damaturu.

 

Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Yaɗa Labarai da Al’adu, Abdullahi Bego, ya ce za a sayi buhunan wake 1,780 na kilo 50, tare da rabawa mata man girki, murhunan da ba sa hayaki, kayan girki da sauran kayayyakin da za su taimaka musu wajen bunƙasa sana’arsu.

 

Haka kuma, gwamnatin ta amince da kashe Naira miliyan 364.5 domin sayo injinan niƙa 1,000 kirar Yamaha GX390 domin rabawa jama’a.

 

Bugu da ƙari, majalisar ta amince da aiwatar da ayyuka da hidimomi da suka kai Naira biliyan 73.32, waɗanda suka haɗa da sayen kayan aikin noma, gina tituna, gidaje, kasuwanni da sauran ayyukan more rayuwa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!