Labarai
Gwamnatin Najeriya ta kafa kwamitin da zai nemo sahihan bayanan da ya sanya aka sace daliban DAPCHI
Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamitin mai mutum 12 don tabbatar da fito da sahihan bayanan da ya sanya aka sace daliban makarantar Sakandaren DAPCHI dake jihar Yobe su 110.
Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya bayar, a babban birnin tarayya Abuja a Talatar nan, inda ya bayyana cewa mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya ne zai kula da kwamitin.
Ya kara da cewa kwamitin, zai samu jagorancin jami’in rundunar sojin kasar nan mai mukamin Manjo Janar da kuma shugaban Kwalejojin horas da sojojin kasa da na sama da na ruwa.
Sannan ya ce sauran mambobin kwamitin sun hadar da wakili daga hukumar leken asiri ta kasa da wakili daga hukumar tsaro ta sojin kasar nan sai kuma wakili daga rundunar yan sandan kasar nan da wakili daga hukumar tsaro ta farin kaya, da kuma wakili daga hukumar tsaro ta civil defence.
Ministan ce cikin kwamitin dai akwai wakilai daga gwamnatin jihar Yobe da kuma wakilai daga ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.
Alhaji Lai Muhammad ya kara da cewa cikin ayyukan kwamitin akwai lalubo hanyoyin da za’a bi wajen kubutar da yan matan na DAPCHI da kuma hanyoyin da za’a bi wajen kaucewa aukuwar irin hakan a nan gaba.
Ya kuma tabbatar da cewa za’a kaddamar da kwamitin ne a gobe Laraba, inda kuma ake sa ran zai gabatar da rahoton sa a ranar 15 ga watan Maris mai kamawa.