Labarai
Gwamnatin Najeriya ta kare matakin da ta dauka na nada Ahmed Rufa’i Abubakar shugabancin hukumar leken asiri NIA
Gwamnatin Najeriya ta kare matakin da ta dauka na nada Ahmed Rufa’I Abubakar a matsayin sabon shugaban hukumar leken asiri ta kasa NIA.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafofin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka ga manema labarai Asabar din da ta gabata a birnin tarayya Abuja.
Ya ce abin takaici ne matuka yadda wasu kafafen yada labaran Najeriya su ka bari ‘yan siyasa suna amfani da su domin biyan bukatun kansu.
Malam Garba Shehu ya kara da cewa babu wani jami’I da ya da ce da wannan mukafi da ya kai Ahmed Rufa’I Abubakar domin kuwa ya rike mukamai manya-manya a hukumar kafin ya bar aikin a kashin kansa bayan da ya samu mukamin darakta a majalisar dinkin duniya.
Babban mai baiwa shugaban kasar shawara ya kuma musanta cewa sabon shugaban hukumar ta NIA ya bar aikin ne sakamakon gaza cin jarabawa da ya yi har sau biyu, yana mai cewar idan mai magana wawa ne majiyin ta ba wawa bane.