Labarai
Gwamnatin Niger ta nemi haɗin gwiwa da Dangote domin haƙa da hada-hadar Mai

Gwamnatin jihar Naija ta nemi aikin haɗin gwiwa da matatar man fetur ta Dangote domin haƙowa da kuma hada-hadar ɗanyen mai da aka gano a Tekun Bida da ke jihar.
Gwamnan jihar Umar Bago ya bayyana aniyar gwamnatin tasa ne yayin wani jawabi da ya yi a bikin baje-kolin kasuwanci da aka gudanar a Minna babban birnin jihar.
Umar Bago ya siffanta albarkatun ɗanyen man da aka gano jihar na da shi a matsayin tikitin cigaban tattalin arzikin jihar ta Neja.
Rahotanni sun bayyana cewa wani bincike da aka gudanar a 2023 ne ya gano rijiyoyin mai 17 da za a kasuwancinsa a jihar, inda aka ƙiyasata cewa za a iya kasuwancinsa na tsawon shekara 70.
You must be logged in to post a comment Login