Labarai
Gwamnatin Nijeriya ta bukaci NLC data janye daga yajin aikin da take shirin shiga
Gwamnatin Nigeriya ta bukaci kungiyar kwadago ta kasar NLC da ta janye batun shiga yajin aiki da ta shirya yi a gobe Laraba.
Ministan kwadago da samar da aikin yi Chris Ngige ne ya bukaci hakan lokacin da ya gayyaci gwamnan babban bankin kasa CBN da shugabannin kungiyar kwadago domin tattaunawa kan batun a ofishinsa.
kungiyar kwadago ta kasa NLC ta fara shirin tafiya yajin aiki a gobe Laraba ne, biyo bayan halin da yan Najeriya ke ciki na rashin kudi a hannun su da kuma karancin man fetur.
Tun a baya dai gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emiefile ya gayyaci shugaban kungiyar kwadago na kasa Joe Ajero domin ya yi masa kan halin da ake ciki ga me da matsalolin da suka lissafa.
Rahoton;Madeena Shehu Hausaw
You must be logged in to post a comment Login