Connect with us

Labarai

Gwamnatin Sojin Burkina Faso ta rushe jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyi

Published

on

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta rushe jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyi a ƙasar biyo bayan dakatar da su a shekarar 2022, sannan kuma za a miƙa duka ƙadarorinsu zuwa ga gwamnatin ƙasar, kamar yadda kafar gwamnatin ƙasar RTB TV ta ruwaito.

Rahotonni sun bayyana cewa, gwamnatin ta amince da dokar rushe jam’iyyun ne a zaman majalisar zartarwar ƙasar, wanda shugaban sojin mulkin soji Ibrahim Traore ya jagoranta.

Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Pingdwende Gilbert Ouedraogo ya ce an ɗauki matakin ne bayan nazarin da aka yi kan rahoton binciken da aka gudanar domin inganta harkokin gwamnatin ƙasar, kamar yadda kafar Lefaso.net mai zaman kanta ta ruwaito.

Kafin juyin mulkin watan Satumban 2022 a ƙasar, akwai jam’iyyun siyasa kusan 100, inda guda 15 a ciki suke da wakilai a majalisar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!