Ƙetare
Gwamnatin sojin Mali ta dakatar da gidajen talabijin biyu mallakin Faransa daga gabatar da wasu rahotanni

Gwamnatin mulkin sojin Mali ta dakatar da wasu gidajen talbijin biyu na Faransa a ƙasar daga bayar da rahotonnin ayyukan masu iƙirarin jihadi.
Hukumar da ke kula da kafafen yaɗa labaran ƙasar, ta ce shirye-shiryen da gidajen biyu suka yaɗa sun ƙunshi cewa zargin cewa masu iƙirarin jihadi na dab da shiga Bamako, babban birnin ƙasar.
Haka ma an zargi kafafen biyu da ƙaryar cewa gwamnati ta hana sayar da man fetur.
A watannin baya-bayan nan, masu iƙirarin jihadi na kai hare-hare kan tankokin dakon mai da ke ɗauko man fetur zuwa Mali, lamarin da ya haifar da ƙarancinsa a faɗin ƙasar.
Masu iƙirarin jihadin sun kuma ƙwace iko da wasu yankunan arewaci da gabashin Mali, duk kuwa da wanzuwar sojojin hayar Rasha a ƙasar.
A shekarar 2020 ne dai sojoji suka ƙwace mulki a Mali a wani juyin mulki, tare da alƙawarin maido da tsaro a ƙasar.
Sai dai bisa ga alama har yanzu matsalar na neman gagarar kundila.
You must be logged in to post a comment Login