ilimi
Gwamnatin Sokoto ta dakatar da wasu shugabannin makarantu

Gwamnatin jihar Sokoto ta dakatar da wasu shugabannin makarantu shida bisa zargin rashin bin doka da kuma karbar kudade ba tare da izini ba dangane da sakamakon jarabawar karamar sakandare JSS.
Kwamishian Ilimi a matakin farko da na Sakandare na jihar, Ahmad Ila ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na Ma’aikatar Ilimi, Ibrahim Iya ya fitar, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.
Kwamishinan ya kuma ce gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wani jami’in da aka samu da laifi.
Domin magance zarge-zargen, kwamishinan ya kafa kwamitin bincike mai mutane biyar karkashin jagorancin Farfesa Mustapha Tukur.
An umurci shugabannin makarantun da aka dakatar da su miƙa dukkan ayyukan gudanarwa ga mataimakan shugabanninsu da ke kula da harkokin gudanarwa nan take.
Har ila yau, ma’aikatar ta jaddada kudirinta na tabbatar da ɗa’a, gaskiya da riƙon amana a fadin makarantun gwamnati a jihar.
You must be logged in to post a comment Login