Labarai
Gwamnatin Sokoto ta yi taruka jin ra’ayin jama’a kan kasafin kuɗi

Gwamnatin Jihar Sokoto, ta ƙaddamar da tarukan jin ra’ayoyin jama’a a mazabu uku na jihar domin shirin kasafin kuɗin baɗi.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, taron da aka gudanar a Tambuwal da Tangaza da Gwadabawa, ya haɗa Sarakunan gargajiya da ‘yan majalisu da kungiyoyin matasa da na mata da kuma na masu bukata ta musamman domin tantance bukatun kowa.
Kwamishinan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Dakta Abubakar Zayyana, ya ce shirin na daga cikin manufar gwamnan jihar, Ahmad Aliyu na tafiyar da mulki a buɗe tare da tafiya da jama’a, wanda zai mayar da hankali kan bangarorin ilimi da kiwon lafiya da na samar da ababen more rayuwa da rage talauci a jihar.
You must be logged in to post a comment Login