Kiwon Lafiya
Gwamnatin taraya ta ranci fiye da naira bilayan 6 daga asusun yan fansho
Gwamnatin tarayya ta ranci fiye da Naira biliyan 6 daga cikin asusun ‘yan fansho da ya kai fiye da Naira biliyan 8.
Mai rikon mikamin babban daraktan hukumar hukumar ‘yan fasho ta kasa PENCOM Hajiya Aisha Umar ce ta bayyana hakan a Abuja cewa gaba kidayan kadarorin ‘yan fasho ya haura fiye da Naira Tiriliyan 8 kawo karshen watan Nuwamban bara.
A cewar, Hajiya Aisha Umar a karshen shekarar da ta gabata fiye da kashi 70 cikin 100 na kadarorin ‘yan fasnho gwamnatin tarayya ta rance su yayin da ta sanya su cikin asusun bunkasa zuba jari na kasa wanda ya sanya ya kai fiye da Niara tirilan 6.
Haka zalika asusun na ‘yan fasnho ya saka jari cikin hukumar jari ta kasa da ya kai kashi fiye da 60 cikin 100.
Mai rikon rikon mukamin babbar darakatar ta ce hukumar ta PENCOM na cigaban da tuntunbar masana da za si kawo cigaba a hukumar don bunkasa asusun na ‘yan fasho ta kasa.