Labarai
Gwamnatin Tarayya da Kawu Sumaila suna shirin inganta aikin Noma

An gudanar da taron bita da fadakarwa ga masu ruwa da tsaki a fannin Noma dangane da sabon aikin gyaran manyan Dam guda Uku da bada tallafin kayan amfanin aikin Gona.
Manoma sama da Dubu Biyu ake sa ran za su amfana da bunkasa harkokin Noman Damuna da Rani a yankin Kano ta Kudu, ta cikin shirin da Sanatan Kano ta Kudu AbdulRahman Kawu Sumaila ya samar tare da hadin gwiwar cibiyar harkokin noma ta kasa da kasa IITA, da tallafin kudaden bunkasa aikin noma da yaki da zaizayar kasa da kiyaye lafiyar muhalli wato Ecological Fund, na gwamnatin Tarayya karkashin ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya, suka samar.
Taron bitar wanda ya kunshi dumbin manoma da jami’an su, da masu ruwa da tsaki a fannin Noma da suka fito daga kananan hukumomin Kano ta Kudu Wanda aka gudanar da shi a nan Kano, ya maida hankali wajen bayyana alfanun da Manoma da dama da suka fito daga yankin zasu samu , musamman ma ta inganta Noma da gudanar da shi ka’in da na’in cikin Rani da Damina ba tare da samun tsaiko ba, Wanda zai taimaka wajen rage yawon ciranin da matasan yankunan ke tafi ya yi jihohin Kudancin kasar nan.
Da ya ke jawabi jami’in mulki da gudanarwa na cibiyar harkokin noma ta kasa da kasa IITA, Ado Rabo Shu’aibu, ya bayyana cewa, taron bitar zai taimaka matuka.
Shi ma a nasa bangaren Daraktan kula da yaki da gurbata muhalli na kasa karkashin shirin tallafin kudaden kiyaye lafiyar muhalli da zaizayar kasa ta tarayya Ecological Fund, Surajo Muhammad Yusuf , ya ce, gwamnatin Tarayya ta sha alwashin bunkasa abubuwa da dama ta cikin shirin wanda zai taimakawa Manoma da kuma inganta tattalin arziki.
Shi kuwa Turakin Karaye Hakimin Karaye, Alhaji Abdullahi Aminu, ya ce masarauta ta yi murna da samun shirin wanda suke da tabbacin zai kawar da Talauci a tsakanin matasa tare da samar musu da aiyyukan yi.
Aikin ana sa ran Manoma manya da ƙanana dubu biyar ne za su amfana da shi, wanda zai bunkasa Dam din Kafin Chiri da Tiga da Karaye , kana ya samar da Injinan ban-Ruwa , da kayan amfanin Noma don tabbatar da dorewar Noman Rani bayan kammala na Damina.
You must be logged in to post a comment Login