Connect with us

Labaran Kano

Za’a dawo da ma’aikatun casar Shinkafa a Kano -Nanono

Published

on

Gwamnatin tarayya  ta sha alwashin farfado da kuma inganta  ma’aikatun casar shinkafa 17 dake nan jihar Kano, tare da samar da sabon tsarin aikin noma na zamani a jihohin Kano da Bauchi nan ba da dadewa ba.

Ministan noma Alhaji Sabo Na Nono, ne ya bayyana haka a yau, a wani taron masu ruwa da tsaki a harkokin Noma da ya gudana tsakanin sa da manoma a dakin taro na Coronation Hall, dake fadar gwamnatin jihar Kano, don samar da ingantaccen tsarin aikin noma na zamani tare da Samar da wadataccen abinci a kasa baki daya.

Alhaji Sabo Na Nono, yace tsohon tsarin da ake amfani dashi na Noma yana cike da kalubale kasancewar a kididdigga kasar nan tana da manoma miliyan 70, amma kwararrun masana na noman zamani da ake dasu a fannin na noma  dubu goma 14 ne daga cikin Miliyoyin manoma.

Don haka gwamnatin tarayya zata fito da shirye -shirye a fadin kasa gaba daya a kananan hukumomi 632, wanda za’a samar da cibiyoyin bunkasawa da sarrafawa wato (Service centres) ga manoman kasar nan.

A nasu bangaren, manoma  da suka halarci taron, ta bakin Alhaji Mukhtari Saleh da Mustapha Halilu sun bayyana babban kalubalen da ake fuskanta a tsarin noma, wanda matukar gwamnatin bata samar da gyara ba ko mafita za ayi ta samu koma baya a bangaren Noma a kasar nan ,musamman ga kananan manoma.

Wakilin mu Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito mana cewa dumbin manoma, da kungiyoyin su ne suka halarci taron a yau tare da gabatar da bayanai, da tambayoyi ga ministan noman don samar da kyaykyawar hanyar inganta Noma a kasar nan tun daga tushe tare da zamanan tar dashi.

RUBUTU MASU ALAKA:

Babu yunwa a Najeriya: Nanono

Za’a fadada gidan abincin N30 zuwa kananan hukumomi 44 na Kano

Shugaban kasa ya damka Amanar biliyan 183 a hannun Kanawa

Shugaban kasa ya damka Amanar biliyan 183 a hannun Kanawa

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,906 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!