Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya na kalubalantar babban jojin Abuja kan karar tsohon dan Majalisa Faruk Lawal
Gwamnatin tarayya ta shaidawa kotun daukaka kara shiyyar Abuja ce wa matakin da babban jojin Abuja ya dauka na mika saurarar karar zargin cin hanci da rashawa da ake yiwa tsohon dan majalisar tarayya Farouk Lawal zuwa hannun wasu alkalai daban daban da cewar ya karya doka.
Faruk Lawal dai ya fada cikin zargin badakalar cin hanci ne lokacin da yake shugaban kwamitin wucin gadi da majalisar ta kafa domin bincikar batun cire tallafin mai da gwamnati ta yi a shekarar 2012.
Inda aka zarge shi da karbar dala dubu dari shida da ashirin a matsayin toshiyar baki daga shugaban wani kamfanin mai Mr Femi Otedola.
Mai shari’a Yusuf Halilu na babbar kotun tarayya da ke Abuja wanda shi ne aka sake mika wa shari’ar ya yanke hukunci tun a ranar 17 ga October shekarar bara inda ya yi watsi da bukatar gwamnatin tarayya na a sake maida shari’ar hannun mai shari’a na farko da ya fara saurarar ta.
Sai dai lauyan da ke kare gwamnati a shari’ar Chief Adegboyega Awomolo ya sake shigar da wasu korafe-korafen har guda uku akan hukuncin da mai shari’a Halilun ya yanke.
Inda ya ce sake maida shari’ar hannun mai shari’a na yanzu wanda a baya har an kusa yanke hukunci, ba wai kawai za a kirashi ba dai-dai ba illa iya saba dokar shari’a