Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Emefiele ya isa gida bayan shafe kwanaki 151 a hannun jami’an tsaro

Published

on

Tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya CBN, Mista Godwin Emefiele, ya isa gidansa da ke birnin tarayya Abuja, bayan da wata babbar kotun Abuja ta bayar da belinsa.

Emefiele ya shafe kwanaki 151 a hannun jami’an tsaro.

Babbar kotun tarayyar da ke zamanta a yankin Maitama ta bayar da umarnin a sake shi daga gidan yari, duk da rashin amincewar da babban lauyan gwamnatin tarayya, da hukumar yaki da cin-hanci da rashawa EFCC suka yi.

A hukuncin da mai shari’a Olukayode Adeniyi ya yanke, ta bayar da umarnin a saki tsohon gwamnan babban bankin ga lauyoyinsa, duk da cewa ta umarce shi da ya miƙa dukkan takardun tafiye-tafiyen sa na kasashen waje.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!