Labarai
Gwamnatin tarayya na shirin ayyana dokar ta-baci a fannin lafiya

Gwamnatin tarayya ta ce za ta ayyana dokar ta-baci a ɓangaren lafiya a faɗin Najeriya sakamakon ƙalubalen da iskar Gas da dangogin sa ke haifarwa na dumamar yanayi.
Ministan muhalli Balarabe Lawal, ne ya bayyana hakan a birnin tarayya Abuja , a wani taron masu Ruwa da tsaki da Majalisar masana muhalli da kiwon lafiya ta kasa EHCON ta shirya kan kalubalen rashin lafiya da ake samu dalilin gurbata muhalli.
Da ya ke jawabi a yayin taron , Ministan wanda babban sakatare a ma’aikatar Mahmud Kambari, ya wakilta a taron ya ce matsalar ta wuce duk yadda ake tunani don haka gwamnatin tarayya ta ga dacewar ayyana daukar matakin gaggawa don magance matsalar.
Haka kuma, gwamnatin ta ce, za ta hada kai, da dukkanin masu ruwa da tsaki, musamman ma masana’antu da kamfanoni na zirga -zirga don ganin an samar da matakan da suka dace wajen amfani da Gas.
You must be logged in to post a comment Login