Labarai
Gwamnatin Tarayya na shirin tattaunawa don dakile yunkurin yajin aikin ASUU

Gwamnatin Tarayya za ta kira taron tattaunawa na musamman domin dakile yiwuwar tsunduma yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i ASUU.
Ana sa ran shugabannin kungiyar za su kira taron majalisar koli NEC, wanda zai yanke hukuncin ko ASUU za ta tsunduma yajin aikin ko a’a, bisa sakamakon tattaunawar da gwamnati za ta yi.
Wani babban mamba a majalisar kolin ta NEC a kungiyar ASUU, wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya zargi gwamnati da yin jinkiri da gangan domin hana kungiyar ɗaukar mataki.
Ya ce bayan ganawar gwamnati, ASUU za ta gudanar da nata taron NEC domin yanke mataki na gaba.
Idan ba a manta ba dai, wa’adin da ASUU ta bai wa gwamnati ya kare a ranar Asabar din da ta gabata.
You must be logged in to post a comment Login