Kimiyya
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da aikin samar da wutar Solar mai ƙarfin Megawatt 1.5 da Injin MRI a NOHDALA

Gwamnatin tarayya, ta ƙaddamar da aikin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana watau Solar mai ƙarfin Megawatt 1 da ɗigo 5 da Kuma na’urar gwajin hoton Ƙwaƙwaf ta MRI samfurin TESLA 1.5 a Asibitin ƙashi na Dala da ke Kano.
Manajan Daraktan hukumar samar da wutar Lantarki a yankunan karkara da ƙananan birane ta tarayya Dakta Abba Abubakar Aliyu, ne ya jagoranci bikin ƙaddamarwar a yau Alhamis.
A jawabinsa yayin taron, shugaban hukumar, ya bayyana cewa, gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta dauki nauyin aikin samar da wutar ne domin magance matsalolin rashin wadatacciyar wutar lantarki a asibitin.
Ya ce, “La’akari da yadda wutar lantarki ke da matsaloli a faɗin Najeriya da kuma rashin tabbacinta, hakan ta sanya ɗaukar matakin don sauƙaƙa matsalar.”
A nasa ɓangaren shugaban Asibitin ƙashin na Dala, Dakta Isah Nuruddeen, ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa ƙaddamar da aikin ya na mai cewa, zai taimaka wajen sauƙaƙa wa marasa lafiya musamman ma wajen rage yawan kudin da asibitoci ke karɓa daga wajensu.
“Kun sani cewa, a baya-bayan nan, akwai Asibitocin da suke yawan samun saɓani da ƴan uwan marasa lafiya saboda tsadar aiki wadda ta samo asali daga yadda kuɗin wuta da man da muke zubawa a injina suka sabbaba saboda duk ayyukanmu sai da wuta.
Haka kuma, muna samun matsala da kamfanin wutar lantarki tun bayan da suka mayar da mu tsaron Band A, wutar ta yi tsada sosai kuma ba ta samuwa yadda ya kamata, amma bisa ƙaddamar da wannan aiki muna da yaƙinin cewa waɗannan matsaloli in Allah ya yadda sun zama tarihi,” in ji Dakta Isah Nuruddeen.
Kamfanin mai na Najeriya NNPCL, ne ya samar da na’urar gwajin hoton Ƙwaƙwaf din ta MRI yayin da ita kuma hukumar samar da wutar Lantarki a yankunan karkara da ƙananan birane ta tarayya za ta samar da wutar lantarkin ta Solar mai ƙarfin Megawatt 1 da ɗigo 5.
You must be logged in to post a comment Login