Labarai
Gwamnatin tarayya ta ɗage shirinta na janye tallafin man fetur

Gwamnatin tarayya ta sanar da ɗage shirinta na janye tallafin man fetur da kudiri aniyar yi a tsakiyar shekarar nan.
Ƙaramin ministan man fetur Timipre Sylva ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin a Abuja, yayin wanin taron masu ruwa da tsaki.
Daga cikin mahalarta taron ganawar akwai shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmad Lawan da ministar kuɗi kasafi da tsare-tsare Hajiya Zainab Ahmad.
You must be logged in to post a comment Login