ilimi
Gwamnatin tarayya ta amince da sauya wa UNIABUJA suna

Gwamnatin tarayya, ta amince da sauya sunan jami’ar birnin tarayya Abuja watau UniAbuja zuwa jami’ar Yakubu Gowon.
Ministan yada labarai Mohammed Idris, ne ya bayyna hakan a ganawar da manema labaran fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala zaman majalisar zartaswa da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a yau Litinin.
Ministan, ya ce, an sauya wa jami’ar sunan ne domin girmamawa ga tsohon shugaban kasar nan Janar Yakubu Gowon mai ritaya wanda a watannin baya ya yi bikin cikarsa shekaru 90 da haihuwa.
Ministan yada labarai Mohammed Idris, ya kara da cewa, za a tura bukatar sahale sauyin sunan ga majalisar tarayya domin neman amincewarta.
You must be logged in to post a comment Login