Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Mun sauya sunan kwamitin kar-ta-kwana mai yaki da corona – Boss Mustapha

Published

on

Gwamnatin tarayya ta amince da sauya sunan kwamitin karta kwana dake yaki da cutar Covid 19 zuwa kwamitin da zai rika bibiya akan al’amuran da suka shafi cutar ta Corona.

Sakataren Gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin Boss Gida Mustapha ne ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Wannan na zuwa ne bayan da aka cika shekara guda da barkewar cutar ta Corona a fadin kasar nan.

A Cewar Boss Mustapha Gwamnatin tarayya ta amince ya cigaba da Jagorantar Kwamitin daga nan zuwa karshen shekarar da muke ciki.

Boss Mustapha ya ce kwamitin zai sanya idanu ne kan dakile cutar a fadin kasar nan tare da daukar matakan kariya domin kawo karshen cutar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!