Labarai
Gwamnatin tarayya ta ayyana jibi Juma’a a matsayin ranar hutu

Gwamnatin tarayya, ta ayyana ranar Juma’a mai zuwa a matsayin ranar hutu domin bukukuwan murnar zagayowar haihuwar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba, ta hannun babbar sakatariyar ma’aikatarsa, Dakta Magdalene Ajani.
Tunji-Ojo ya taya al’ummar musulmin Najeriya da ma duniya baki daya murnar zagayowar wannan rana.
Haka kuma ya bukaci Musulmi da su yi koyi da kyawawan dabi’u da zaman lafiya da kaunar da tawali’u da juriya da tausayi kamar yadda Manzon tsira ya ke da su, ya na mai cewa, bikin Maulidi abu ne da ke ba da dama wajen karfafa dankon zumunci da inganta zaman lafiya.
You must be logged in to post a comment Login